1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

Sudan ta zargi wasu kasashe da tallafa wa 'yan tawaye

Abdourahamane Hassane
November 6, 2024

Jakadan Sudan a birnin Paris na Faransa ya ki kiran da a kawo karshen yakin basasa a kasarsa.

Hoto: AFP

 Jakadanya yi kira ga kasashen duniya da su  matsa lamba kan kasashen da ke ba da taimako ga dakarun gaggawa na (RSF) masu rura wutar rikici. Jami'in diflomasiyyar ya bukaci kasashe musamman Hadaddiyar Daular Larabawa da Chadi da  Sudan ta Kudu da Habasha da Yuganda da su daina tallafa wa mayakan sa kai.  Ya kuma yi nuni da cewa Sudan ta tunkari Faransa don shiga tsakanin Sudan da Chadi. A jiya Talata Sudan ta sanar da cewar ta shigar da kara a gaban kungiyar Tarayyar Afirka a kan kasar Chadi,inda ta zargi makwabciyarta da samar da makamai da harsasai ga dakarun  RSF.