Sudan: Hankula sun kwanta a Darfur
January 19, 2021Gwamnatin rikon kwarya a babban birnin kasar Khartoum ce ta tura da rukunin sojoji zuwa yankin, inda hukumomi suka nuna fargabar karin zubar da jini.
Tun dai a ranar Asabar din da ta gabata ce dai rikici ya barke a tsakanin makiyaya labarawa da kuma mambobin wata kungiyar kabilar a El Geneina da ke yammacin Darfur, wanda ya yi sanadin rayukan kimanin mutane 155, yayin da wasu 130 suka jikkata. Haka kuma mutane kimanin dubu hamsin suka rasa matsugunansu sanadiyar rikicin. Rikicin dai ya zo a dai-dai lokacin da dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke shirin janyewa daga yankin baki daya.
Tuni dai mahukunta yammacin Darfur, suka sanya dokar hana zirga-zirga yayin da jami'an soji suka isa yankin da ma wasu jihohin don dawo da kwanciyar hankali.