Matar da ta kashe mijinta ta sami sassaucin kotu
June 26, 2018Talla
An sami matar da yanzu ke da shekaru goma sha tara da laifin kisan ne bayan da ta dabawa mijin na ta wuka a lokacin da ya ke tsakiyar yi ma ta fyade tare da taimakon wasu 'yanuwansa da suka rike ta, bayan ta ki amincewa ya tara da ita a auren dole da aka yi mata.
Hukuncin kotun na farko ya ja hankulan duniya inda kungiyoyi masu adawa da hukuncin kisa dama wasu da masu zaman kansu da suka yi ta fafutuka don ganin kotu ta yi adalci na yin watsi da hukuncin na kisa.