1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gasar Bundesliga ta Jamus ta kara zafi

Mouhamadou Awal Balarabe SB
November 4, 2024

Sudan na ci gaba da taka rawar gani a wasanin neman tikitin shigar gasannin kwallon kafan Afirka da duniya duk da yaki da take fama da shi. Alexander Zverev na Jamus ya mamaye Ugo Humbert na Faransa a wasan karshe.

Jamus I Bundesliga - Borussia Dortmund da RB Leipzig
Borussia Dortmund da RB LeipzigHoto: Leon Kuegeler/REUTERS

 

Yaya-karama Borussia Dortmund ta yi nasarar kauce wa tarkon da RB Leipzig ta dana mata a mako na tara na Bundesliga, bayan shan kashi uku a jere a hannun Real Madrid da Augsburg da kuma Wolfsburg a gasar cin kofin kwallon kafar Jamus. A wannan karon dai, BvB da ke fama da rikici da raunukan 'yan wasa ta samu nasara da ci 2-1 a kan RB Leipzig da a karon farko da barar da wasanta tun bayan fara kakar-wasanni. Sai dai duk haka, RB Leipzig ta ci gaba da zama a matsayi na biyu na teburin Bundesliga da maki 20. Ita kuwa Borussia Dortmund takoma matsayi na biyar, amma a yawan maki 16, tana tafiya kafada da kafada da zakaran kwallon kafar Jamus Bayer Leverkusen, sakamkon kunnen doki da ta yi da Stuttgart 0-0. A nata bangare, Eintracht Frankfurt ta murkushe 'yar baya ga dangi Bochum da ci 7-2, lamarin da ya sa ta haye mataki na uku da maki 17.

Karin Bayani: Labarin Wasanni: Bayern ta yi kunnen doki

Eintracht Frankfurt da BochumHoto: Malte Ossowski/SVEN SIMON/picture alliance

Ita kuwa, Yaya-babba Bayern Munich ta mamaye Union Berlin da ci 3-0 a filin wasa na Allianz Arena, wanda hakan ya sa zama kungiya daya tilo da ba taba dokewa ba ya zuwa yanzu. Hasali ma dai, 'yan wasan Munich sun ci wasa na uku ke nan a jere,  kuma ta kasance ita kadanta a saman teburin Bun desliga da maki 23. Kwallon da Hary Kane ya ci munti shida bayan dawo hutun rabin ne ya fi daukar hankali, saboda a lokacin da muka kawo muku sharhin wannan wasa a ranar Asabar ne aka fara ganewa cewar bakin alkali ya bushe wa Union Berlin

A sauran sakamakon kuwa, Holstein Kiel ta doke Heidenheim da ci daya mai ban haushi, yayin da St Pauli ta bi Hoffenheim har gida kuma ta doke ta da ci 2-0. Su kuwa Wolsburg da Augsbrug sun yi kunnen doki 1-1

Manchester United da SouthamptonHoto: IMAGO/Shutterstock

A sauran manyan lig na kasashen Turai, A Ingila, babau yabo babu fallasa ga Manchester United a karkashin kocinta na rikon kwarya Ruud van Nistelrooy inda ta tashi 1-1 da Chelsea, lamarin da ya sa ta ci gaba da kasancewa a matsayi na goma sha uku a gasar Premier bayan makonni goma. Sai dai  kunnen dokin ya bai wa Chelsea damar hayewa matsayi na hudu da maki 18, daidai da Arsenal ta biyar da Aston Villa ta shida, da aka doke  ci 4-1 a Tottenham. Sai dai Liverpool ta yi amfani da wannan damar wajen dawo da martabarta sakamakon nasarar da ta samu na takwas a wasanni goma, inda ta haye saman teburi da maki 25 bayan da ta doke Brighton da ci 2-1. Ita kuwa Manchester City tana a matsayi na biyu da maki 23 , yayin da Nottingham Forest ke a matsayi na uku da 19 bayan lallasa West Ham da ci 3-0.

La LigaHoto: Joan Monfort/AP Photo/picture alliance

A Spain kuwa, Barcelona ta mamaye abokiyar hamayyarta Espanyol  da ci 3-1 a ranar Lahadi, tare da karfafa matsayinta na jagorar gasar La Liga a mako na goma sha biyu da maki 33. Wannan nasarar da ke zama ta sha daya a wasanni 12, ta sa Barcelona yin ratar maki tara a kan babbar abokiyar hamayyarta Real Madrid da ke a matsayi na biyu da 24, wacce aka dage wasanta a Valencia saboda mummunar ambaliyar ruwa da birnin ya fuskanta.

A Faransa, Paris Saint-Germain ta samu ratar maki shida a saman teburin Ligue 1 bayan da ta doke Lens da ci 1-0, yayin da ta ci gaba da nuna rashin kwazo kwanaki kadan kafin haduwa da Atletico Madrid a gasar zakarun Turai. Ita kuwa Monaco tana a matsayi na biyu bayan da ta ba  Angers kashi da ci 1-0.

Hoto: Noah Wedel/IMAGO

Kungiyar kwallon kafar mata ta jami’ar Western Cape da ke Afirka ta Kudu ta samu gurbin shiga gasar zakarun Afirka ta 2024 bayan ta lashe kofin COSAFA, lamarin da ke zama farau ga wata kungiya da ta fito daga jami’a. Duk da cewa ta sha kashi a wasan rukunin a hannun Green Buffaloes, amma dai Kungiyar UWC ta samu nasarori a kan manyan kungiyoyi irin su Ongos FC da ci 3-0. A wasan karshe ma dai, bayan 1-1 da Gaborone United a mintuna 90 na wasa, UWC Ladies ta yi nasara a bugun daga kai sai mai tsaron gida 9-8.

Mai tsaron gidan matan Jami'ar Western Cape Siphesihle Dlamini na daya daga cikin manyan 'yan kungiyar, inda ta taimaka wajen kiyaye ragarta. Yayin da kocin mata Thinasonke Mbuli ta taka muhimmiyar rawa a nasarar da suka samu, sakamakon inganta yanayin horo da zaburar da 'yan wasa ga ba da himma, wanda ya ba da gudummawa ga ci gaban kungiyar zuwa ga rukunin mata na gasar zakarun Afirka.

Har yanzu muna Afirka, inda duk da yakin basasa da yake ci gaba da daidaita kasar Sudan, kuma yake jefa al'ummar kasar cikin mawuyacin hali, amma kuma kungiyar kwallon kafar kasar na samun gagarumar nasara da ba a taba gani ba. Yanzu haka ma, akwai yiwuwar kasar ta iya samun tikitin shiga gasar kwallon kafa ta neman cin kofin nahiyar Afirka ta shekarar 2025 da ma gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026.

'Yan wasan SudanHoto: Kenzo Tribouillard/AFP/Getty Images

'Yar tseren kasar Kenya Sheila Chepkirui mai shekaru 33 ta ba da mamaki inda ta lashe gudun fanfalaki na birnin New York a cikin sa'o'i biyu da mintuna 24 da dakiko 35 a ranar Lahadi, lamarin da ke zama babbar nasararta ta farko a duniya. Abin da ya fi daukar hankali, shi ne yadda Chepkirui ta yi nasara kawar da 'yar uwanta Hellen Obiri da ta lashe gudun New York a 2023 kuma ta samu lambar tagulla a gasar Olympics ta Paris a bazara, a lokacin da suka durfafi mitocin karshe. Saboda hake ne, 'yar gudun fanfalakin ta nuna gamsuwa da irin tsarinta na horo, saboda da kwalliyarta ta mayar da kudin sabulu. Ita dai, Sheila Chepkirui ta samu matsayi na shida a gudun fanfalaki na London a cikin bazara bayan ta haska a bara a Berlin, inda ta zo a matsayi na biyu a cikin sa'oi biyu da mintuna 17 da kuma dakika 49 (2h17mn49s).

Yanzu kuma sai fagen tennis, inda cikin sauki bajamushe Alexander Zverev da ke da matsayi na uku a duniya ya lashe gasar Masters 1000 ta birnin Paris, bayan da ya samu nasara a kan dan wasan Faransa Ugo Humbert da ci 6-2, 6-2 a wasan karshe.  Wannan dai, shi ne karo na bakwai da Zverev mai shekaru 27 ya lashe kofin Masters 1000 a duniya, amma na farko a Paris. Amma dai, wannan shi ne karon farko da Humbert ya fafata wasan karshe na Masters 100, kuma ya kasa zama dan Faransa na farko da ya lashe gasar Paris tun bayan wandaa Jo-Wilfried Tsonga ya lashe a 2008. Amma dai, Hugo Humbert ya yi nasarar yin waje road da Carlos Alcaraz na biyu a duniya da kuma Karen Khachanov.