Sudan: Mayakan RSF sun shiga Wad Madani
December 19, 2023
Talla
Tun watanni takwas da suka gabta dakarun sa kai na RSF suke dannawa Wad Madani babban birnin jihar El Gezira kuma a ranar litinin mayakan suka shiga birnin a cewar rahotanni.
Yaki tsakanin sojoji da RSF ya tilasta wa mutane fiye da miliyan bakwai barin gidajensu yayin da a waje guda halin tagaiyarar da jama'a suka shiga ya haifar da kashe kashen kabilanci a Darfur.