1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

MDD ta damu kan halin da 'yan gudun hijira ke ciki a Sudan

November 3, 2023

A tsukin watanni shida, rayukan mutane 9,000 ne suka salwanta yayin da wasu miliyan shida suka yi kaura daga Sudan; la,arin da majalisar Dinkin Duniya ke cewa bai dace ba.

Sansanin 'yan gudun hijirar Sudan a Thadi
Sudan: MDD ta damu da halin da 'yan gudun hijira ke cikiHoto: ZOHRA BENSEMRA/REUTERS

Yanyin da ake ci gaba da gwabza kazamin fada a yankin Darfurna kudancin Sudan, Majalisar Dinikin Duniyata bukaci da a kara matsa kaimi don rage wa mutane sama da miliyan shida da rikicin da tilasta masu yin gudun hijira radadin wahalhalun da suke ciki.

Karin bayani: Sudan: Al'umma na cikin mawuyacin hali

A tsukin watanni shida rayukan mutane 9,000 ne suka salwanta yayin da wasu miliyan shida suka yi kaura ciki har da miliyan 1,2 da suka bar kasar sai dai duniya ta juya idanuwa kan abin da ke faruwa a zirin Gaza in ji Mamadou Dian Balde dakakatan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR da ke Sudan.

Karin bayani: Matsalar agaji ga mabukata a Sudan

Akalla dai dalar Amurka biliyan guda hukumar ke bukata a karkashin shirinta na kula da wadanda rikicin Sudan ya raba da matsugunensu, sai dai kashi 38 cikin dari na wadannan kudade kadai ne ta samu yayin da bukata ke karuwa a wannan yanki da dama ke fama da talauci.