1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sudan: MDD ta yi tir da harin RSF a kauyen Wad Al-Noura

June 7, 2024

Sakataren MDD Antonio Guterres ya yi tir da Allah wadai da wani kazamin harin da ake zargin rundunar sa kai ta RSF ta kai a wani kauye da ke gabashin Sudan tare da kisan sama da fararen hula 100.

Sudan | Mohamed Hamdan Daglo
Hoto: Ashraf Shazly/AFP

Masu fafutikar dimokuradiyya a Sudan sun bayar da rahoton cewa a ranar Larabar da ta gabata ce dakarun da ke karkashin janar Mohamed Hamdane Daglo suka kai harin da manyan makamai na atilari a kauyen da ake kira Wad Al-Noura da ke yankin Al-Jazira a kudancin kasar.

Baya ma ga halaka fararen hula sama 100, rahotannin na nuni da cewa harin ya yi sanadiyar jikkatar wadansu darurruwan mutane.

Karin bayani: Masar za ta dauki nauyin taron sasanta rikicin Sudan

Antoniyo Guterres ta bakin kakakinsa ya nuna matukar damuwa kan halin kunci da wannan yaki da ya barke a watan Afrilun bara ya jefa miliyonyin al'ummar Sudan, tare kuma da kiran bangaron da ke fada da juna da su ajiye makamai.