1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadarin jirgi ya kashe mutane a Sudan

Abdul-raheem Hassan
January 3, 2020

Mutane 16 ne aka tabbatar da mutuwarsu, bayan da jirgin saman sojojin Sudan ya fado a yammacin yankin Dafur mai fama da rikicin kabilanci.

Sudan Flugzeugabsturz
Hoto: Getty Images

Rahotanni sun nunar da cewa ma'aikatan jirgin su bakwai sun mutu, kana wasu alkalai uku da kuma fararen hula takwas ciki har da kananan yara da wani jami'in hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya da iyalansa na daga cikin wadanda suka rasa rayukansu yayin hadarin.

Ba a tabbatar da musabbabin faduwar jirgin nan take ba, amma yankin da jirgin ya yi hadarin na fama da rikicin kabilanci. Sama da mutane 40 sun mutu wasu da dama sun jikkata a wani artabu tsakanin kabilu da ba sa jituwa da juna a yankin a baya-bayan nan.