Sudan na fuskantar matsalar jin kai mafi girma a duniya
November 16, 2025
Boulos ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP cewar rikicin kasar Sudan, bangaren jin kai matsala ce mafi girma a duniya a yau.
Kazalika ya bayyana cewar yana fatan nan bada jimawa ba za a cimma maslaha ta diflomasiyya a tsakanin bangarorin dake gaba da juna.
Tun bayan barkewar rikicin Sudan a watan Afrilun 2023, yakin yi yi sanadiyar salwantar rayukan dubban fararen hula tare da raba kusan miliyan 12 da muhallansu.
Da yake bayani a game da karbe iko da birnin El-Fasher da dakarun RSF suka yi, Massad Boulos ya ce,
"A makonni biyu ko uku da suka gabata, mun ga faya-fayan bidiyon abin da ya faru, wadannan ayyukan ta'addancin sam ba za a amince da su ba. Dole ne a dauki mataki cikin sauri."
Washington ta bukaci bangarorin da ke rikici da juna a Sudan da su gagauta hawa teburin sulhu don kawo karshen wannan matsalar.
Karin Bayani: Majalisar Dinkin Duniya za ta tura tawagar bincike birnin el-Fasher na Sudan