Tsohon shugaban Sudan a gaban kuliya
July 21, 2020Talla
Daga laifuffukan da ake tuhumarsa akwai yiwa dokokin tsarin mulkin kasar karan tsaye kamar yadda guda daga cikin lauyoyin da suka shigar da karar ya shaidawa manema labarai a wannan Talatar. Tsohon shugaba al-Bashir mai shekaru 76 zai gurfana gaban shari'ar ne tare da wasu mutane 60 da suka hada wasu wadanada suka rike mukaman mataimakan shugaban kasar da tsoffin ministoci da kuma tsoffin gwamnoni a lokacin gwamnatinsa.