1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Soji sun tarwatsa masu zanga-zanga

Binta Aliyu Zurmi
February 7, 2022

Masu zanga-zanga Sudan sun sake fantsama a kan tituna, inda suke ci gaba da nuna kin amincewar su da matakin karbe iko da soji su ka yi a a bara, sai dai soji sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla wajen korarsu.

Sudan | Pro-Demokratie-Demonstranten trotzen dem harten Vorgehen nach dem Putsch
Hoto: DW

Zanga-zangar ta yau dai ta ci karo ne da turjiyar jami'an tsaro inda suka y amfani da karfi wajen tarwatsa su gami da watsa musu hayaki mai sa hawaye a lokacin da suka tunkari fadar gwamnati da ke birnin Khartoum.

Al'umma a kasar dai na ci gaba da nuna fushinsu tun bayan hambarar da mulkin farar hula da janar Abdel Fattah al-Burhan ya jagoranta a watan Oktoban shekarar bara.

Kawunan 'yan kasar ta Sudan na a rarabe, a yayin da wasu ke kin amincewa da matakin sojojin, a karshen makon da ya gabata daruruwan masu goyon bayan sojojin sun gudanar da ta su zanga-zangar.