1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cimma yarjejeniyar tafiyar da mulki a Sudan

Abdourahamane Hassane
July 17, 2019

Sojoji da ke yin mulki a Sudan da kuma masu yin bore a karon farko sun cimma wata yarjejeniya ta raba madafun iko, bayan da aka kwashe watanni da dama ana kai ruwa rana tsakanin sasan biyu.

Sudan Khartoum | Friedensgespräche
Hoto: picture-alliance/AA/M. Hjaj

An dai kwashe tsawon lokaci ana tattaunawa tsakanin wakilan kungiyoyin da masu mulkin kafin a kai ga cimma yarjejeniyar, wacce ta  tanadi cewar sojojin za su yi watanni 21 suna yin mulki na wuccin gadi. Sannan  farar hula su karba a tsawon watanni 18 na gwamnatin rikon kwaryar.