1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Sojojin gwamnati sun kara samun galaba

March 22, 2025

Rundunar sojin Sudan ta yi nasarar karbe iko da karin wasu yankuna na babban birnin kasar, Khartoum, a wani mataki da ke zama babban tarnaki ga mayakan RSF da ke hankoron kawar da gwamnatin da MDD ta amince da ita.

Sudan | Vorsitzender des Souveränen Rates des Sudan | Abdel Fattah al-Burhan
Hoto: AFP

Bayan galabar sake karbe iko da fadar shugaban kasa da sojojin na Sudan suka yi a ranar Juma'a, a wannan Asabar, dakarun gwamnatin sun yi nasarar korar mayakan RSF a cikin garin Kahrtoum inda manyan ofisoshin gwmanati ke da zama.

Mai magana da yawun sojojin Birgediya Janar Nabil Abdullah ya ce jami'ansu sun tsaurara tsaro a muhimman wuraren da suka hada da babban bankin Sudan da gidan adana kayan tarihi na kasa da sauran muhimman gine-ginen gwamnati da ke cikin kwaryar birnin Khartoum. Babban sojan ya ce a sakamakon hakan, abokan aikinsa sun yi nasarar bindige mayakan RSF masu yawa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW