Sudan ta amince da shirin sulhu da mayakan RSF
January 23, 2026
Sabon daftarin da aka yi wa lakabi da “watanni shidan farfadowa” Yariman Saudiya Muhammad Bin Salman ne ya nemi Amurka ta tsoma baki don gabatar da shi da samun tabbacin aiwatar da shi sau da kafa. Faisal Bin Farhan, ministan harkokin wajen Saudiya ya yi karin bayani kan dagewar Saudiya na tabbatar da kawo karshen yaki a Sudan.
“Tabarbarewar da ayyukan agaji su ka yi sakamakon ci gaban yaki a Sudan, ya jefa kimanin mutane miliyan 15 cikin yunwa a kasar da ada ake yiwa kirari da rumbun abincin kasashen larabawa. Idan bamu gaggauta kawo karshen wannan annobar ba, to mu kanmu yunwar za ta shafe mu. Abun takaici ne ace su kansu jagororin yaki a Sudan za su ci gaba da yin fatali da taye tayin tsagaita wuta da kudurorin neman yin sulhu har sau shida cikin shekaru uku na yaki. Saudiya ita ta fara gabatar da irin wannan tayin. A wannan karon, tare da hadin gwiwa da Amurka, muna gabatar da wani sabon tayin da muka gabatar da muke fatan zai samar da zaman lafiya da kwanciya hankali a Sudan.”
Wannan sabon daftarin da ya nemi tsagaita wuta na watanni shida ba tare da gindaya sharudda ba, da tilasta wa kasashen da ke tsoma baki a cikin rikicin na Sudan janye hannayensu .
Bugu da kari, sabon daftarin zaman lafiyar na Sudan ya nemi kowane bangare ya ci gaba da tafiyar da iko a yankunansa ba tare da kai sabbin hare haren ba. Tuni dai Sojojin Sudan suka sanar da cewa sun fara nazari kan wannan sabon daftarin.
Tun daga watan Afrilun 2023 ne dai yaki ya barke tsakanin ɓangarorin biyu. Jakadan Amurka na musamman a kasar Sudan Masoud Bulos yace wannan ita ce dama ta karshe da Amurka za ta ba wa jagororin yakin na Sudan ko dai su dakatar da yaki ko su kuka da kansu:
“Mun jima muna rokon bangarori biyu da su tsagaita wuta kan dalilai na agaji da tausaya wa mutanen da suka shiga cikin halin tagaiyara, amma har yanzu shiru. Wannan sabon kudirin da muke gabatarwa ba zabi bane tilas ne. Baza mu bari a ci gaba da zubar da jinin bayin Allah haka kawai ba. Dole ne cikin gaggawa a dauki matakan kawo karshen matsalar ayyukan agaji a kasar.”
Masharhanta na ganin cewa, wannan matakin da Saudiya ta dauka, na hada karfi da Amurka don kawo karshen yaki a Sudan gami da takunkumin tattalin arziki kan duk kasashen da ke da hannu a rikicin, ba ya rasa nasaba da irin raba garin da Saudiyar ta yi da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa a Yemen.
Yakin ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane, tare da raba wasu kusan miliyan 11 da matsugunansu