1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yunkurin yin juyin mulki a Sudan

September 21, 2021

Gidan talabijin na Sudan ya sanar da cewa an yi yunkurin juyin mulki a kasar, wanda bai yi nasara ba. Gidan talabijin din da ke a birnin Khartoum, ya ce an yi yunkurin karbe iko da ita a safiyar Talatar nan. 

Sudan I Politik I Abdallah Hamdok
Hoto: Getty Images/AFP/E. Hamid

Sai dai gwamnatin wucin gadi ta kasar ta ce jami'an tsaro sun shawo kan lamarin  kuma sun kaddamar da bincike kan wadanda ake zargi da kitsa juyin mulkin da bai yi nasara ba.


Kamfanin dillancin labarai na Sudan din SUNA, ya ruwaito mai magana da yawun rundunar sojojin kasar Birgideiya-Janar Al-Tahir Abu Haja na cewa bayan dakile juyin mulkin, sun kamo dukkanin sojojin da suka yi yunkurin karbe ikon. 


Ministan yada labaran kasar Hamza Baloul ya zargi tsofaffin jami'an gwamnatin Sudan ta Omar- al-Bashir da ta rushe da yunkurin juyin mulkin.