Sudan ta janye daga yankin Abyei
June 2, 2012
Jami'ai daga rundunar sojin Sudan sun sanar da cewar Sudan ɗin ta janye jami'an 'yan sandanta daga yankin Abyei mai arziƙin man fetur da take taƙaddamar mallakarsa tare da Sudan Ta Kudu. Tuni dama Sudan Ta Kudu wadda ita ma ke da'awar mallakar yankin na Abyei ta janye dakarunta daga yankin. Tunda farko dai Sudan ta ce za ta ci gaba da jibge rundunar 'yan sanda ta musamman mai ƙunshje da dakaru 169 a yankin na Abyei domin bada kariya ga rijiyoyin man fetur na Difra, amma ta janye wannan ƙudirin a wannan Jumma'ar sakamakon matsin lamba daga al'ummomin ƙasa da ƙasa. A yanzu dai akwai wata rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya mai ƙunshe da dakarun ƙasar Ethiopia 3,800 dake kula da sha'anin tsaro a yankin. Hakanan a Jumm'ar nan ce Sudan Ta Kudu ta gabatarwa kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya buƙatar sanyawa Sudan takunkumi bisa zargin da tace na jefa bama-bamai a yankunan ta.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman