1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sudan ta katse huldar diflomasiyya da kungiyar IGAD

January 16, 2024

Gwamnatin mulkin sojin Sudan ta maida kakkausar martani tare da dakatar da alaka da kungiyar raya kasashen gabashin Arfika IGAD, bisa zargin katsa landan a harkokin cikin gida da kuma gayyatar bangaren RSF Kampala.

Wani Sojin Rundunar RSF dauke da tutar Sudan
Wani Sojin Rundunar RSF dauke da tutar SudanHoto: Hussein Malla/AP Photo/picture alliance

Cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin waje ta fitar, gwamnatin Janar Al Burhan ta bayyana cewar kungiyar ta IGAD da nuna wariya da kuma bambanci maimakon ta maida hankali kan sulhunta rikicin da ke addabar Sudan.

A makon da ya gabata ne kungiyar raya kasashen gabashin Afrika IGAD ta aike da goron gayyata ga Mohamed Hamdan Daglo, zuwa taron kungiyar a Uganda, inda tuni ya amince da bukatar hakan.Wannan mataki ya harzuka gwamnatin kasar ta Sudan, wanda ya zo watanni tara (9) bayan fara yakin Sudan tsakanin shugaban mulkin sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da tsohon mataimakinsa Hamdan Daglo.

A halin yanzu ma dai, bangaren gwamnatin Sudan na rasa iko da wasu muhimman wuraren, inda a gefe guda Hamdan Doglo ke fadada ikonsa wajen gudanar da ziyarce-ziyarce a wasu manyan biranen nahiyar Afrika.

Wata kungiya da ke tattara alkaluman yakin ta ce mutane sama da 13,000 suka rasa rayukansu, yayin da alkaluman Majalisar Dinkin Duniya ya ce mutane sama da milyan 7.5 sun rasa matsugunansu.