1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta Kudu: Adawa da takunkumin hana makamai

Abdullahi Tanko Bala | Salissou Boukari
February 6, 2018

Daruruwan mazauna Juba babban birnin Sudan ta Kudu sun gudanar da zanga-zanga domin nuna adawa da takunkumin hana sayar wa kasar makamai da Amirka ta yi, inda suka kira da ta sauya shawarar da ta dauka. 

Sudan Jubel über Friedensabkommen
Masu zanga-zanga a Sudan ta KuduHoto: picture-alliance/dpa/P. Dhil

Masu zanga zangar kenan matasa maza da mata wadanda suka yi cincirindo a kofar ginin hukumar kiyaye zaman lafiya a Sudan ta Kudu inda suka gabatar da takardar koke wanda suka yi korafin cewa takunkumin hana sayarwa Sudan ta Kudu makamai da Amirka ta yi sam bai dace ba. Majalisar sarakunan Sudan ta Kudu ita ce ta jagoranci zanga-zangar. Shugaban sarakunan Taban Luka shi ya karanta wasikar kafin ya mika ta ga ofishin jakancin Amirka yana mai cewa: "Gaban kai da Amirka ta yi wajen daukar wannan hukunci na hana sayarwa gwamnatin Jamhuriyar Sudan ta Kudu makamai, a matsayin mu na sarakuna muna gani wani mataki ne na sare wa gwamnati gwiwa yadda abokan gaban kasar nan a cikin gida ko a waje za su ga gwamnatin bata da katabus, yadda za su sami damar yi mata juyin mulki."

Mayaka 'yan tawaye a Sudan ta KuduHoto: Reuters/G. Tomasevic

Zanga-zangar dai ta biyo bayan sanarwar da gwamnatin Amirka ta bayar ne a makon da ya wuce cewa ta sanya takunkumin hana sayarwa da Sudan ta Kudu makamai a wani mataki na matsawa gwamnatin kawo karshen yakin da ake fama da shi a kasar. Sarakunan dai sun yarda cewa ana yaki a Sudan ta Kudu to amma sun yi Allah wadai da matakin hana sayar da makaman suna cewa hakan wata barazana ce ga kasar a matsayinta na mai cin gashin kanta: " Muna kira ga gwamnatin Amirka ta sake nazarin wannan mataki saboda a matsayin mu na jama'ar Sudan ta Kudu a shirye muke mu fadawa Amirka cewa abin da kika yi ba zai taimaka wajen samun zaman lafiya a Sudan ta Kudu ba."

Masu zanga zangar wadanda suka fusata sun yi ta jifar ginin rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya. Tun shekaru hudu da suka wuce ne dai ake yaki a Sudan ta Kudu bayan da shugaba Salva Kiir ya raba gari da tsohon mataimakinsa kuma madugun 'yan adawa a yanzu Riek Machar, shekaru biyu kacal bayan da kasar ta sami mulkin kai.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani