Sudan ta Kudu: An sako ma'aikatan agaji da aka sace
April 30, 2018Talla
Wannan dai ba shi ne karon farko da ma'aikatan agaji ke fuskantar barazanar kai hare-hare a yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula a Sudan ta Kudu ba. Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin kasar ya lamushe rayukan ma'aikatan agaji 100 tun watan Disamban shekara ta 2013, a yanzu dai tuni aka wuce da ma'akatan da sukia kubuta a jitgin Red Cross zuwa Juba babban birnin kasar Sudan ta Kudu.