Sudan ta kudu na fiskantar tashin hankali
January 6, 2012MDD tace dubun-dubatan mutane suka tsere wa tashin hankalin kabilanci da ake yi a kasar Sudan ta kudu. A 'yan makwannin nan ana fiskantar tashin hankali a jahar Jonglei, inda wasu kabilu suka kona gidajen abokan gaban su da yawa, kana suka wawushe wani asibiti wanda kungiya agaji ta Doctors Without Borders ke amfani da shi. Wakiliyar bada agaji ta MDD a Sudan ta kudu Lise Grande, tace mai yuwa an hallaka daruruwan mutane a fadar ta kabilanci da ta faru. Kana ta yi gargadin cewa karancin abinci ya yi muni a yankin da yan gudun hijarn suke. Sudan ta kudu dai tun a watan Julin bara ta samu yanci, amma zaman lafiya bai samu ba, inda take kokarin farfado da tattalin arzikinta, wanda yanzu ya dogara kusan a kan manfetru kacokan. Masu lura da al'amuran sabuwar kasar suka ce, akwai alamun gabar kabilanci da matsalar kiwon shanu za su iya sa Sudan ta kudu ta koma wata kasar da al'amuran mulki suka wargaje.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu