Riek Machar na fuskantar zargin cin amanar kasa
September 26, 2025
Machar wanda tun a watan Maris din wannan shekara yake fuskanta daurin talala, a karon farko ya gurfana a gaban kotu yana fuskantar tuhume-tuhume da suka hada da kisan kai da cin amanar kasa gami da laifukan cin zarafin bil'Adama, wadanda ke da nasaba da tashin hankalin da aka yi yankin Nasir da ke arewacin kasar a farkon wannan shekara da ya shafi mayakan sa kai na White Army yan kabilar Nuer.
A farkon watan nan ne shugaban kasar Salva Kiir ya dakatar da Machar bisa wata ayar doka, da ya dangana da matsalar tsaron kasar. Matakin dai ya kawo cikas ga gwamnatin hadin kan kasar da aka kafa karkashin yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar ta 2018.
Omara Joseph, jami'in kungiyar kare hakkin bil'Adama ta Sudan ta Kudu, ya shaida wa tashar DW cewa tsare mataimakin shugaban kasar da ake ci gaba da yi na da fuskoki da dama, kazalika ya cacaki matakin hana 'yan jarida shiga zama shari'ar da ake yi.
" Wannan wata alama ce da ke nuna cewarSudan ta Kudu za ta iya fuskantar kalubalenta, kuma duk wanda ya taka doka to doka za ta yi aiki a kanshi, wannan lokaci ne da kasashen duniya za su kawo mana dauki domin, menenen dalilin hana wasu 'yan jarida shiga zaman shari'ar sai wasu 'yan jaridun cikin gida kawai? duniya ya kamata ta san hakikanin abin da ke faruwa a wannan shari'ar.''
Masu saka idanu a al'amuran da ke gudana a tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa na cewar irin wannan kan-kangewar da hana 'yan jarida rawar gaban hantsi a game da wannan shari'ar ka iya nuna cewar shari'ar na da nasaba da bita da kullin siyasa kamar yadda wasu ke cewa.
Wannan shari'ar dai ta sake haifar da rikicin kabilanci wanda dama ke tsakanin kabilun Nuer ta Reik Machar da kuma masu goyon bayan Shugaba Kiir na Dinka. Tabitha Nyantin 'yar gwagwarmaya a kasar ta ce shugabannin biyu kamata ya yi su mayar da fifikonsu ga hadin kan kasa.
"Muna da kabilu da yawa a kasar nan, kuma shugabanni sun fito daga kabilu dabaM-dabaM, Idan har ba su canza tunaninsu ba, wannan banbanci ba zai bar mu mu ci gaba ba kamar makwabciyarmu Kenya"
To a yayin da ake ci gaba da wannan shari'ar, gwamnatin hadin kan kasa ke cikin rudani, fargabar ba a kan mataimakin shugaban kasar da makusantansa kawai ta tsaya ba har ma da makomar Sudan ta Kudu kanta. A shekarar 2018 ce aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya da aka kawo karshen yakin basasa na shekaru biyar wanda ya lakume dubban rayukan fararen hula.