Sudan ta Kudu ta amince da bukatar Trump na jibge fursunoni
July 12, 2025
Kasar Sudan ta Kudu ta amince da bukatar Amurka, Ruwanda kuma ta ce tana ci gaba da tattaunawa da Trump, yayinda Najeriya ta yi fatali da bukatar Washington.
Karin bayani: Najeriya ta bijire wa muradin Trump na jibge mata bakin hauren Venezuela
Amurka dai ta bujiro da shirin aike wa da fursunoni da bakin haure dake jibge a kasar zuwa kasashe, maimakon maida su kasashensu na asali. Amurka ta aike da daruruwan fursunonin Venezuela zuwa kasashen Costa Rica da El Salvador da kuma Panama, inda kuma take neman fadada aikinta na jigilar wadancan mutane da ta kira bata-gari zuwa Afirka da Asia da kuma Turai.
Karin bayani: Kotun kolin Amurka ta ba wa Trump damar aiwatar da munufarsa ta korar baki
Babban jami'in da ke kula da iyakokin Amurka Tom Homan ya sanarwa da manema labarai cewa gwamnatin Trump na ci gaba da tattaunawa da kasashe da dama domin waiwatar da wannan manufa ta dakile bakin haure shiga kasar ta Amurka.
Batun bakin haure na daga cikin batutuwan da shugaba Trump ya tattauna da wasu shugabannin Afirka biyar da suka gana da shi a fadar White House wadanda suka hada da na kasashen Liberiya da Senegal da Guinea-Bissau da Mauritaniya da kuma Gabon.