Sudan ta Kudu ta kafa dokar hana fita bayan zanga-zanga
January 17, 2025Hukumomin Sudan ta Kudu sun sanya dokar hana fita dare a Juba babban birnin kasar, bayan wata zanga-zanga da ta rikide zuwa sace-sacen kayayyaki mallakin 'yan kasuwan Sudan. A wata hira da ya yi da gidan talabijin na kasar, babban sufeto janar na 'yan sandan Sudan ta Kudu Abraham Manyuat ya ce an dauki wannan mataki ne don kare dukiyoyin al'umma, a daidai lokacin da sabuwar zanga-zanga ke neman yaduwa zuwa sauran biranen kasar.
Karin bayani: Salva Kiir zai yi tazarce a Sudan ta Kudu
A yammacin ranar Alhamis ne aka gudanar da zanga-zanga a birnin Juba domin nuna adawa da kisan da aka yi wa 'yan kasar Sudan ta Kudu 29 a garin Wad Madani na Sudan da ke fama da yaki. 'Yan sanda sun yi harbe-harbe don tarwatsa masu zanga-zanga, amma ba babu alkaluma game da asarar rayuka da aka samu.
Karin bayani: MDD: Rikici ya ki cinyewa a Sudan ta Kudu
Duk da cewa kura ta lafa a Juba, sai dai yawancin shaguna sun kasance a rufe bayan da aka jibge sojoji da 'yan sanda a manyan titunan birnin. Sai dai, an fara wata sabuwar zanga-zanga a wani banbare na Juba da kuma garuruwan Bor, Aweil da Wau.