1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta Kudu ta jirkirta lokacin zabe

Abdul-raheem Hassan
August 4, 2022

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta jinkirta zaben da aka shirya yi a karon farko tun bayan samun 'yancin kai a 2011, saboda gwamnatin rikon kwarya ta sanar da tsawaita wa'adin mulki zuwa wasu shekaru biyu nan gaba.

Sudan ta Kudu
Hoto: Jok Solomun/REUTERS

Wannan mataki ya fara sa wasu kashen waje fara nuna tababa kan makomar kasar da ta sha fama da tashe-tashen hankula a shekarun baya.

Amma gwamnatin Sudan ta Kudu ta ce sun dauki matakin tsawaita mulkin rikon kwarya ne zuwa 2024 don tinkarar kalubalen da ke hana kasar aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya, biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 2018 na kawo karshen yakin basasar da aka shafe shekaru biyar ana yi, wanda ya yi  sanadin mutuwar mutane kusan 400,000.