Sudan ta Kudu: Yarjejeniyar sulhu ta karshe
September 13, 2018Talla
Shugaba Salva Kiir na kasar Sudan ta Kudu da jagoran tawayen kasar Riek Machar sun rattaba hannu kan yarjejeniyar karshe ta kawo karshen yaki da kasar ta sami kanta a ciki, a wani taron da aka yi a Addis Ababa na kasar Habasha, bayan tattaunawar makonni biyu.
Cikin watan jiya ne aka amince da samar da gwamnatin riko a kasar ta Sudan ta Kudu, inda za a maida Mr. Machar matsayinsa na mataimakin shugaban kasa. Sai dai duk da matsayin da bangarorin suka cimma a ranar Laraba (12.09.2018), da dama daga cikin masu kallon lamarin daga waje, na shakku kan nasarar dorewar hakan.
Jaririyar kasar ta fada yakin basasa ne a shekara ta 2013, bayan zargin yunkurin juyin mulki da Shugaba Salva Kiir ya yi wa Riek Machar, wato tsohon mataimakin nasa.