Sudan ta Kudu za ta fuskanci takunkumi
July 10, 2014Kungiyar Tarayyar Turai ta saka takunkumin tafiye-tafiye da rufe asusu ajiya manyan jami'an soji biyu na kasar Sudan ta Kudu, bisa hannun da suke da shi na tashe-tashen hankulan da suka hargitsa kasar.
Wata sanarwar kungiyar ta ce gobe Jumma'a za a bayyana sunayen mutanen, lokacin da takunkumin zai fara aiki. Matakin na Tarayyar Turai ya zo bayan kwashe watanni ana fafatawa tsakanin dakarun da ke biyayya wa Shugaba Salva Kiir da na tsohon mataimakinsa Riek Machar.
Rikicin ya janyo mutuwar kimanin mutane dubu 10, yayin da wasu fiye da milyan daya da rabi suka tsere daga gidajensu, abin da ya haifar da matsaloli masu yawa na harkokin jinkai.
Tun farko Amirka ta nemi bangarorin da ke rikici a kasar ta Sudan ta Kudu su dauki matakan dakile yakin basasan da ya gobe tun cikin watan Disamba. Shekaru uku da suka gabata kasar ta balle daga Sudan.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu