1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta Kudu za ta tura sojoji Kwango

Suleiman Babayo ZMA
December 28, 2022

Sudan ta Kudu za ta tura dakaru Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango cikin dakarun hadin gwiwa na kasashen gabashin Afirka.

Sudan ta Kudu | Manyan habsoshin soja
Sojojin Sudan ta KuduHoto: AFP via Getty Images

Kasar Sudan ta Kudu za ta tura sojoji 750 zuwa gabashin kasar Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango, domin aiki tare da dakarun kasashen yankin gabashin Afirka. Mai magana da yawun rundunar sojan kasar ya tabbatar da haka.

A 'yan watannin da suka gabata kazamin fada ya barke tsakanin dakarun kasar ta Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango da mayakan 'yan tawaye na kungiyar M23, abin da ya janyo kungiyar kasashen yankin gabashin Afirka tura dakarun hadin gwiwa domin dakile rikicin, inda tuni dakarun kasashen Kenya da Yaganda suka isa.

Sojojin 750 na Sudan ta Kudu sun kwashe watanni shida suna samun horo na musamman gabanin tafiyar da za su yi.