1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

Sudan za ta dakatar da hukumar UNITAMS

November 17, 2023

Gwamnatin rikon kwaryar Sudan ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta gaggauta kawo karshen ayyukan da hukumarta ta UNITAMS ke yi a kasar da yaki ke neman daidaitawa.

Sudan na neman raba gari da hukumar MDD da ke kasarHoto: Gueipeur Denis Sassou/AFP

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa a cikin wata wasika mai dauke da saka hunnun ministan harkokin wajen Sudan Ali Sadek, mahukuntan kasar sun ba da tabbacin cewa sun kudiri aniyar yin hulda mai inganci da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya amma kuma sun bukaci da a gaggauta kawo karshen ayyukan hukumar UNITAMS a kasar.

Karin bayani:  Sudan: MDD ta damu kan halin da 'yan gudun hijira ke ciki

An dai kafa wannan hukuma mai ma'aikata akalla 400 a shekarar 2020 da nufin dafa wa gwamnatin rikon kwaryar Sudan don dawo da kwanciyar hankali da zaman lafiya a kasar bayan boren shekarar 2018 wanda ya yi awon gaba da gwmanatin wancan lokaci.

Karin bayani:  Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ya yi murabus

To sai dai mahukunkan Sudan sun shiga takun saka da hukumar da suke zargi da gaza cimma manufofin da aka kafata domin su biyo bayan barkewar rikicin kasar a ranar 15 ga watan Afrilun da ya gabata. Wannan takun saka ne ma dai ya kai wakilin Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar Volker Perthes yin murabus daga mukaminsa a watan Satumban da ya gabata bayan da gwamnatin Abdel Fattah al-Burhane ta bayyana shi a matsayin mai kara rura wutar rikici tsakaninta da rundunar sa kai ta RSF.