SiyasaAfirka
An sake artabu a tsakanin sojoji da masu bore a Sudan
December 30, 2021Talla
Jami'an tsaron Sudan sun fesa wa masu zanga-zanga barkonon tsohuwa a birnin Bahri. Hukumomi sun dauki matakin domin tarwatsa masu boren da suka so kutsa kai ta wata gada da ta hada birnin na Bahri da babban birnin kasar Khartoum da jami'an tsaro suka toshe.
Duk da cewa matakin ya tirsasa wa sojoji mayar da mulki ga Firaminista Abdalla Hamdok bayan juyin mulkin watan Oktoba, lamarin ya janyo mutuwar mutane 48 a sakamakon artabun da sojoji ke yi da masu zanga-zangar.
Tun da farko hukumomi a Sudan sun jibge karin jami'an tsaro a birnin Khartoum sannan suka makala na'urorin daukar hoto a wuraren da ake yawan yin zanga-zanga.