Sudan ta zargi Abu Dhabi da taimaka wa RSF a rikicin Darfur
April 10, 2025
Talla
Koken Sudan ga kotun ICJ wanda aka fi sani da Kotun Duniya, na da alaka da hare-haren da suka shafi kabilanci da dakarun Sojojin Sama na Rapid Support Forces da kawayensu na Larabawa 'yan bindiga suka yi a kan wadanda ba Larabawa ba a 2023 a lardin Darfur.
Kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa dai ta sha karyata wannan zargi tare da alakanta shi da siyasa. A watan Janairu ne Amurka ta ayyana hare hare a kan 'yan kabilar Masalit a matsayin kisan kare dangi.
Khartoum na zargin Abu Dhabi ta bai wa RSF da ke fada da dakarun gwamnati tsawon shekaru biyumakamai, zargin da MDD da Amurka suka yi amana da shi duk da cewar HDL ta karyata.