1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Tsaikon rattaba hannu kan rabon mulki

Mahmud Yaya Azare
July 12, 2019

An dage rattaba hannu kan daftarin yarjejeniyar rabon mulki tsakanin majalisar sojin wucin gadi da masu fafutuka sakamakon wani yunkurin juyin mulkin da sojojin suka ce sun bankado.

Sudan | Militärregierung PK Putschversuch  vereitelt
Hoto: picture-alliance/AA

Yunkurin juyin mulkin da sojojin suka ce wasu kananan hafsoshin soji da jami'an tsaro masu aiki da wadanda suka yi ritaya suka kitsa shi, ya kai ga chafke  jami'ai 16 da suka hada da hafsoshin soji da jami'an leken asiri inji Jagoran kwamitin tsaro na gwamnatin soji ta wucin gadi Janaral Jamal Omar Ibrahim.

“Jami'an tsaro sun yi nasarar bankado wani yunkurin juyin mulki da wasu kananan hafsoshin sojin da jami,an leken asiri suka shirya da nufin kawo cikas ga yarjejeniyar da sojoji da shugabannin farar hula suka cimma na kafa gwamnatin hadaka, yarjejeniyar da za ta share fagen mayar da kasarmu kan mulkin farar hular da 'yan kasarmu ke hankoran ganin ya tabbata.”

'Yan adawa masu fafutuka a SudanHoto: picture-alliance/AA/O. Erdem

Sojojin dai basu yi karin haske kan rana da lokacin da aka yi wannan yunkurin juyin mulkin ba, lamarin da ya sanya Ahmad Okasha, daya daga cikin kusoshin masu fafutukar, ya zargi sojojin da jan kafa wajen kafa gwamnatin hadakar.

Ana dai rade radin cewa wasu daga cikin manyan hafsoshin sojin kasar basa jin dadin irin babakeren da mataimakin shugaban majalisar wucin gadin Muhammad Doglo Humaity ke yi a madafan ikon kasar wanda ake ganin yana da burin mulkin kasar, ko da kaki ko kuma ya tsaya takara a matsayin farar hula.

A yanzu haka dai ana sa ran a ranar lahadi za a rattaba hannu kan yarjejeniyar rabon mukaman a bikin da ake sa ran shugabannin kasashen Ruwanda da Afirka ta Kudu da Masar,da kuma shugaban Habasha Ahmad Abe wanda ya shiga tsakani don cimma yarjejeniyar za su halarta.

 

.