1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Masu manyan laifuka sun gudu daga gidan kaso

April 26, 2023

Ahmed Haroun tare da wasu tsoffin jigajigai a hambararar gwamnatin Sudan ta Omar El Bechir da ake tuhuma da aikata laifin kisan bil'adama sun tsere daga gidan kason birnin Khartum.

Bildergalerie | Evakuierung von Ausländern aus dem Sudan
Hoto: Spanish Defence Ministry/REUTERS

Yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin sojojin masu biyayya ga gwamnati da dakarun RSF duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma bisa jagorancin Amurka wasu tsoffin jami'ai a gwamnatin Sudan da karin wasu fursunoni sun tsere daga gidan kason da ake tsare da su.

Jami'an sun hadar da Ahmed Haroun da ke tsare tare da tsohon shugan kasar Omar El Bechir wadanda su duka biyu kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC ke nema ruwa a jallo bisa aikata laifin kisan bil'adama a Darfur.  

A wani faifan bidiyo da gidan talabijin din kasar Sudan ya watsa ya nuno Ahmed Haroun din ya na cewa sun share kwanaki tara ne a tsare a gidan kason na Kober dake Khartum kafin su yi ta ransu sakamakon zafafar hare-hare a kusa da inda suke kuma a halin yanzu suna a guri marar hadari. 

To sai dai a daren jiya Talata gwamnatin sojan Sudan din ta sanar da cewa tsohon shugaban kasar Omar El Bachir da aka hambarar a shekarar 2019 na ci gaba da jinya a wani gidan asibiti bisa sa idon jami'an tsaro sannan ta ce ana binciken gano inda Ahmed Haroun din wanda ke da hannu a yakin basasan Darfour ya buya.