Tsoron kisan gilla yayin da RSF ta kewaye el-Obeid
June 29, 2026
Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da kasashen Turai sun shiga damuwa kan yadda yakin Sudan ke ci gaba da lakume rayukan jama'a da ba su ji ba su gani ba.
Birnin el-Obeid na yankin arewacin Kordofan ya dauki hankalin duniya a yanzu bayan da aka gano cewa dakarun RSF na yin tururuwa zuwa cikinsa.
Karin bayani: Yaushe za a daina yaki a Sudan?
Kwamitin sulhu na MDDa ya nuna fargabar cewa birnin el-Obeid da ke hannun sojojin Sudan tun watan Fabarairun bara na fuskantar faruwar makamancin kisan kare dangi da ya faru a birnin el-Fasher, lokacin da dakarun RSF suka kashe fararen hula kimanin 6,000 a cikin kwanaki uku a watan Oktoban 2025, bayan mamaye garin na tsawon watanni 18.
Wannan ya sanya Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yin kira da cewa lallai kada a bari tarihin el-Fasher ya maimaita kansa.
Me ya sa RSF ke son kai wa el-Obeid hari?
Shigar da RSF ta fara yi a garin el-Obeid a kwanan nan, irinta aka gani a wancan lokaci na kisan kiyashi ta hanyar kaddamar mamaya da muggan hare-hare ta kasa. Wannan gari na da mutane kimanin dubu 500,000 da ke tsakanin tsakiyar Sudan da birnin Khartoum da kuma yammacin yankin Darfur. Shi ne ma tungar sojin gwamnatin Sudan, kuma babbar kafa ta shigar da kayan agaji ga mabukata.
Hager Ali, kwararriya a sha'anin siyasa da aikin jarida da bincike a cibiyar GIGA Institute for Global and Area Studies ta Jamus, ta shaida wa DW cewa tarihi ya nuna muhimmanci da kuma tasirin el-Obeid, wanda ba zai taba misaltuwa ba, musamman a fagen shigar da kayan tallaf.
Karin bayani: Duniya ta manta da 'yan gudun hijirar Sudan
A don haka matukar aka yi sakaci har RSF ta kwace garin, babu shakka za a tafka mummunar asara, domin za ta mamaye albarkatun karo na birnin da sauran kayan more rayuwar jama'a da ke jibge a garin. Bugu da kari, nan ne ma cibiyar aikewa da jirage marasa matuka domin kai hare-hare.
Gargadi don guje wa kashe-kashe el-Fasher
Wani rahoton Hukumar Bayar da Agaji da Jin Kai ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA ya ce mutane fiye da 1000 ne aka kashe daga Janairun 2026 zuwa watan Mayun da ya gabata, ta hanyar amfani da jirage marasa matuka a yakin na Sudan.
Sai dai Hager Ali ta ce saukar ruwan sama a damunar bana ka iya takaita barnar da jirage marasa matuka ke yi a kan fararen hula a wannan yaki.
Karin bayani: Yunwa a Sudan ta Kudu na yin barna
A nasa bangaren, tsohon shugaban kungiyar kare hakkin 'dan adam ta duniya Human Rights Watch, Kenneth Roth, ya ce tabbas RSF ta fito da halinta a fili karara, da ke nuna cewa babu abin da ta sa a gaba face kisan dumbun fararen hula ba-gaira-ba-dalili, wannan kuma mummunan zalunci ne ga bil'adama.
Yakin basasar Sudan ya barke ne a watan Afirilun 2023, domin neman kwatar iko tsakanin sojojin gwamnatin Sudan karkashin Janar Abdel Fattah al-Burhan, da kuma dakarun RSF da ke karkashin jagorancin Mohamed Hamdan Dagalo, wanda a kasar aka fi sani da Hemedti.
Sudan, kasa mai arzikin karkashin kasa
Kasar Sudan ta dare gida biyu, inda sojoji suka rike ikon yankin arewaci da tsakiyar kasar, ciki har da Khartoum babban birninta, yayin da RSF ta mamaye yammacin Darfur da kuma wasu bangarorin kudancin kasar.
Karin bayani: Cin-zarafin 'yan gudun hijirar Sudan a Chadi
Sudan, kasa ce mai arzikin man fetur da gwal, ga kuma tarin kasa mai albarkar noma. Amma yanzu ta zama tarkon mutuwa inda ta fuskanci yanayin jin kai mafi muni a duniya in ji Majalisar Dinkin Duniya. Alkaluma sun nuna mutuwar mutane tsakanin 40,000 zuwa 250,000, yayin da fiye da miliyan 14 suka tsere daga gidajensu.