Kin mutumta yarjejeniyar tsagaita a Sudan
May 4, 2023Sojojin da ke biyayya ga manyan hafsoshin sojan Sudan biyu da ke kokawar iko, sun sa kafa sun shure yerjejeniyar tsagaita wutar da aka tsawaita izuwa ranar 11 ga watan Mayu domin samun damar isar da kayan agaji. Masu aiko da rahotanni sun ce an ji karar fashewar bama-bamai da kuma manyan bindigogi, yayin da fadan ke ci gaba da jefa al'umma cikin kuncin rayuwa na katsewar wutar lantarki da ruwan sha da kuma hauhawar farashi da ma karancin man fetur.
Babban kwamishinan kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya Volker Türk ya yi tir da yadda wani jirgin sojoji ya yi luguden wuta a kan wani asibiti da kuma yadda dakarun RSF ke kai hare-hare a unguwannin fararen hula. A yankin Darfur kuwa inda fararen hula suka dauki makamai domin shiga yakin kuwa, kungiyoyin agaji sun nuna takaicinsu kan yadda fada tsakanin kabilun yankin ya yi ajalin mutane 191 tare kuma da kone gidaje masu yawa.