Sudan: Yan RSF sun kashe mutane a asibitoci
October 29, 2025
Talla
Mayakan sa kai na RSF a Sudan sun kashe daruruwan mutane ciki har da marasa lafiya a asibitoci bayan da suka kwace iko da birnin el-Fasher da ke yammacin Darfur a cewar Majalisar Dinkin Duniya da ma'aikatan agaji wadanda suka baiyana munin ta'asar.
Shugaban kungiyar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanon Gebreyesus a cikin wata sanarwa ya ce marasa lafiya 460 da masu jinyar su mayakan RSF sun kashe su a asibitin Saudi da ke el-Fasher babban birnin arewacin Darfur.
Ya ce kungiyar lafiya ta duniya ta kadu matuka da lamarin.
Kungiyar likitoci ta Sudan da ke bin diddigin yakin ta ce mayakan RSF sun kashe duk wadanda suka samu a cikin asibiti har da ma'ikatan jinya da ke kula da marasa lafiyar.