An tarwatsa masu adawa da soji a Sudan
November 7, 2021Talla
Zanga-zangar ta biyo bayan kiran da wata kungiyar kwadago, na bijirewa umarnin gwamnati tare da yin watsi da tayin raba madafun iko da sojoji. Kungiyar kwadon da ta kira zanga-zangar ta taka rawa sosai a zanga-zangar 2018 zuwa 2019 da ya kai ga hambarar da tsohon Shugaban kasar Omar al-Bashir a watan Afrilun 2019.
Masu zanga-zangar sun yi barazanar shiga yajin aiki na tsawon kwanaki biyu fara daga ranar Lahadi. Tun bayan juyin mulkin ranar 25 ga watan Oktoba na shekarar 2021, aka fara zanga-zangar kin jinin mulkin soji a Sudan, akalla mutane 14 ne aka kashe tare da raunata kusan 300, a cewar likitocin Sudan.