1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceSudan

Yaushe za a kawo karshen yakin Sudan?

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 7, 2025

Akwai fargabar ba za a iya kawo karshen yakin da ake gwabzawa a Sudan ba, duk da cewa mayakan RSF da suka kwashe sama da shekaru biyu suna yakar sojojin gwamnatin kasar sun amince da tayin tsagaita wuta.

Sudan | Yaki | Gwamnati | Janar Abdel Fattah al-Burhan | RSF | Mohammed Hamdan Daglo
Rikicin Sudan na sama da shekaru biyu, ya tilasta mutane yin gudun hijiraHoto: NRC/AP Photo/picture alliance

Kwararru dai na ganin babu tabbacin rundunar RSF a shirye take ta aiwatar da sulhun, tare da yin gargadin cewa mayakan na shirin kai munanan hare-hare da nufin kwace iko da birnin el-Obeid da ke kudancin kasar. Gwamnatin da sojoji ke goyon baya, ba ta amsa tayin na al'ummomin kasa da kasa karkashin jagorancin Amurka ba.

Yakin sama da shekaru biyu

Abubuwa masu fashewa sun yi bindiga a Khartoum babban birnin kasar da ke karkashin ikon sojojin gwamnatin. Tun a watan Afrilun 2023 ne, yaki ya sake barkewa a Sudan tsakanin sojojin gwamnatin Janar Abdel Fattah al-Burhan da mayakan RSF karkashin jagorancin tsohon mataimakinsa Mohammed Hamdan Daglo.

Cin kasuwa a fagen yaki a Sudan

01:15

This browser does not support the video element.

A hannun guda Majalisar Dinkin Duniya ta zargi Hadaddiyar Daular Larabawa da bai wa mayakan na RSF makamai, zargin da Daular Larabawan ta yi ta musantawa. A hannu guda kuma, Saudiyya da Masar da Turkiyya da Iran na tallafawa sojojin gwamnati.

Yunkurin samar da zaman lafiya

A yanzu Amurka da Saudiya da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Masar na neman a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, a yakin da ya tarwatsa sama da mutane miliyan biyu tare da haifar da mummunan yanayin agajin jin-kai.