1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan za ta maida hulda da kotun ICC

Binta Aliyu Zurmi
October 18, 2020

Sudan ta bayyanna anniyarta ta maida hulda da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa a yayin wata ziyarar aiki da Fatou Bensouda mai gabatar da kara ta kotun ke yi Sudan.

Niederlande Den Haag |  Fatou Bensouda Chefanklägerin Internationaler Strafgerichtshof (ICC)
Hoto: picture-alliance/AA/A. Asiran

BenSouda wacce ta gana da hukumomin a birnin Khartoum ta tattauna kan batutuwan mika tsoffin jagoran kasar da ake zargi da aikata manyan laifuka a gaban kotun, sai dai da take tsokaci babbar alkalin mai shgar da kara bata bayyana tattaunawa kan batun tsohon shugaban kasar Umar Hassan Albashir ba, wanda kotun ke zargi da aikata manyan lafukan yaki da cin zarafin bil'Adama.

Ko da yake Bensouda ta ce ziyarta a Sudan na nuni da cewar an samu muhimmin sauyi a kasar.