1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Barkewar boren kin jinin gwamnati a Sudan

Abdoulaye Mamane Amadou
November 13, 2021

Duk da tsauraran matakai da hukumomin kasar Sudan suka dauka, masu boren kin jinin gwamnatin mulkin soja sun fito zanga-zanga inda suka yi arangama da jami'an tsaro.

Sudan Port Sudan | Proteste gegen Militärregierung
Hoto: AFP/Getty Images

Jami'an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla don tarwatsa dandazon masu bore da zanga-zanga da suka fito a biranen Khartoum da Omdourman a cigaba da zanga-zangar kin jinin gwamnatin mulkin soja.

Tun a yammacin jiya ne ma dai hukumomi a wannan kasa, suka karfafa matakan tsaro a manyan biranen biyu, a yunkurinsu na dakile boren masu rajin kare gwamnatin farar hular, sai dai masu aiko da rahotanni sun ce har yanzu ana cigaba da zanga-zangar, yayin da masu boren suka kakkafa shingaye a kan tituna.

Zanga-zangar na zuwa ne kwanaki biyu bayan da jagoran juyin mulki a Sudan din Janar Abdel Fattah al-Burhane ya sake nada kansa a matsayin shugaban majalisar rikon kwarya ta kasar bayan da ya rusa ta farar hula a karshen watan Oktoba.