Sudan: Zargin amfani da makamai masu guba
September 29, 2016Talla
Kungiyar kare hakkin jama'a ta kasa da kasa ta Amnesty International, ta ce akwai alamun cewar gwamnatin kasar Sudan ta kai hare-haren makamai masu guba 30 a garin Jebel Marra da ke lardin Darfur, tun daga watan Janairu, kamar yadda kwararru ke zargi.
Kungiyar fafutukar ta kiyasta cewar a kalla mutane 250 ne suka mutu, wadanda ake zargin mutuwar da nasaba da makamai masu guba da aka yi amfani dasu wajen kai hare haren.
A wata sanarwar daya gabatar, jakadan Sudan a Majalisar Dunkin Duniya Omer Dahab Fadl Mohamed, ya ce zargin na Amnesty ba shi da wani tushe, domin Sudan bata mallaki ko wane irin makami mai guba ba.