1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan:Karancin taimakon jinkai a al-Fasher

Mouhamadou Awal Balarabe
December 4, 2025

Mutanen da ke tsere wa tashin hankalin al-Fashir na Sudan ba sa samun taimakon da ya kamata a kan iyakar kasarsu da Chadi sakamakon karancin tallafin kasa da kasa da kungiyoyin jin kai ke fuskanta

Sudan Al-Dabba 2025 | Freiwillige kochen für Geflüchtete aus El-Fasher im Al-Afad-Lager
Hoto: Ebrahim Hamid/AFP

A sansanin wucin gadi da ke kan iyakar Chadi da Sudan, Najwa Isa Adam, mai shekaru 32, tana raba taliya da nama ga yara marayu da suka zo daga al-Fashir, garin da dakarun RSF suka kwace iko a kwanakin baya a Sudan. Najwa ta isa sansanin gari Tine ne a watan Oktoba, amma a yanzu, tana amfani da kudin da wasu 'yan gudun hijira suka bayar domin sayen abinci tare da raba shi ga sabbin zuwa.

Sannan kungiyoyi masu zaman kansu na aiki a garin Tine, ciki har da Médecins Sans Frontières, wacce ke da asibitin tafi-da-gidanka a kan iyaka da kuma karamin sashen marasa lafiya da ke budewa kwana uku a cikin mako. Kimanin yaro daya cikin hudu da ke fama da cutar rashin abinci mai gina jiki ne MSF ta kula da su, duk da kwararar iyalai da ke tserewa daga al-Fashir, in ji Josh Sim, ma'aikacin gaggawa na MSF.

Karin Bayani: Sudan na fuskantar matsalar jin kai mafi girma a duniya

Yara maza da mata a sansanin 'yan gudun hijira na al-Fasha a yankin DarfurHoto: Sarah Vuylsteke/NRC/AP Photo/picture alliance

Najwa Isa Adam, ta ce ga wasu iyalai, tushen abincinsu ya kasance gudummawar da wasu 'yan gudun hijira ke bayarwa.

"Muna rayuwa ne daga taimakon da mutanen Tine na kasar Chadi suke bayarwa da kuma mutane 'yan gudun hijirar Sudan. Matasan garin na hada hannu da ni wajen taimaka wa mutane. Mun kasance kimanin mutane shida ko bakwai kuma muna son taimaka wa 'yan'uwanmu. Wannan aikin agaji ne, sun ba mu abinci kyauta kuma mun yanke shawarar rarraba abincin."

Shirin Abinci na Duniya ya fara rarraba abin sa wa a bakin salati mata masu juna biyu da masu shayarwa da yara 'yan kasa da shekara biyu don kandagarkin cutar rashin abinci mai gina jiki. Amma a kokarin karfafa 'yan gudun hijira ga kaura zuwa wurare mafi aminci, hukumar agajin abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da mafi yawan albarkatun zuwa wasu sansanonin da ke nesa da kan iyakar Sudan da Chadi, in ji wani mai magana da yawunta.

Karin Bayani: Majalisar Dinkin Duniya za ta tura tawagar bincike birnin el-Fasher na Sudan

Iyalai 'yan gudun hijira a sansanin al-Fasha da ke DarfurHoto: NRC/AP Photo/picture alliance

It kuwa Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya na da kashi 38% ne kawai daga dala miliyan 246 da take bukata don magance matsalar 'yan gudun hijirar Sudan a Chadi, a cewar kakakin UNHCR

Nawal Abubakr Abdul Wahab, mai shekaru 49, wacce malamar makaranta ce a al-Fashir, ta ji rauni a hannu a lokacin da ta gudu a watan da ya gabata, amma ba ta samun magani ba har yanzu:

"Babu magani, babu kulawa, babu komai sai bokiti da abubuwan da ba a rasa ba da suka ba mu. Mun fito daga al-Fashir da tufafinmu kawai, ba tare da kudi ba, ba tare da takalma ba, ba tare da barguna ba. Ba mu da komai."

Karin Bayani: Sudan: Rawar kasashen ketere a rikicin da ke faruwa

Tattaunawa da wata 'yar gudun hijira a al-FashaHoto: Sarah Vuylsteke/NRC/AP Photo/picture alliance

A bisa al'ada, sansanin 'yan gudun hijira kamar wanda ke Tine zai iya daukar 'yan gudun hijira na dan lokaci kafin a kaurar da su zuwa sansanonin da ke dauke da tsaro a cikin kasar Chadi. Amma karancin kudaden ya sa ba a samar da isasshen ruwa, ba a samar da tsaftataccen muhalli ga sabbin masu shigowa ba-. 

Ibrahim Mohamed Ishaq, mai shekaru 35, ya isa sansanin wucin gadin ne tare da matarsa ​​da 'ya'yansu mata biyu daga Abu Shouk da ke arewacin al-Fashir, babban birnin Arewacin Darfur. Amma ya ce ya ga yadda mayakan RSF suka harbe 'yan uwansa sama da hudu kafin su yanke shawarar yin hijira.

Karin Bayani: Fafaroma Leo ya yi kiran a dakatar da yakin kasar Sudan

Wasu 'yan gudun hijirar Sudan da suka yi kaura zuwa ChadiHoto: Joris Bolomey/AFP

"Akwai matsaloli da yawa a al-Fashir kuma abin bakin ciki ne domin ana kai hare-hare a kullum, ana kashe mutane, ana korarsu. Sannan akwai 'yunwa, mutane da yawa suna cin Ambaz (abincin dabbobi) da sauransu. Koma wani hali muke ciki, muna godiya ga Allah da muka yi kokari, kuma Allah ya cece mu kuma muka fita lafiya."

Tun bayan da Al-Fashir ya fada hannun rundunar RSF a karshen watan Oktoba bayan watanni 18 na tashin hankali, ana kyautata zaton cewar sama da mutane 100,000 ne suka tsere daga Al-Fashir, a cewar Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Duniya. Kuma kimanin mutane 9,500 ne suka isa Chadi. Sannan MSF ta kiyasta cewa kimanin mutane 180 ne ke ketara iyakar Sudan da Chadi domin zuwa Tine a kowace rana.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani