Sukar matakin hana Visa sabo da Ebola
October 28, 2014Talla
Ministan yada labarai na Saliyo din Alpha Kanu ne ya yi wannan suka inda ya ce matakin ya zamo tamkar nuna wariya da kuma kyama ga al'ummomin kasashen Saliyo da Gini da kuma Laberiya da yawansu ya kai akallah miliyan 24. Tun da fari dai a wannan Talatar ne kasar Ostareliyan ta bayyana cewa ta dakatar da ba da takardun iznin shiga kasarta wato Visa ga wadanda suka fito daga wadandannan kasashe, abun da ta bayyana da cewa matakin dakile shigar bala'in annobar Ebolan zuwa kasarta.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohamadou Auwal Balarabe