Farfado da dimokaradiyya a Burkina Faso
September 21, 2015Yayin taron da suka gudanar a wannan Lahadi karkashin jagorancin shugaban kasar Senegal Macky Sall da takwaransa na Jamhuriyar Benin Thomas Boni Yayi sun bukaci da a dawo da shugaban kasar na rikon kwarya da sojojin suka hambarar a makon jiya kana a yi wa sojojin da suka jagorancin juyin mulkin afuwa. Sun kuma bukaci da a baiwa magoya bayan tsohon shugaban kasar da masu zanga-zanga suka tilastawa ajiye mukamin nasa Blaise Compaore damar tsayawa takara a zaben da za a gudanar a watan Oktoba mai zuwa.
A baya dai mahukuntan kasar ta Burkina Faso sun haramtawa duk wani da ke mara wa Compaore baya tsayawa takara a zabukan kasar da aka shirya gudanarwa domin mayar da kasar bisa tafarkin dimokaradiyya bayan kwashe shekaru 27 karkashin jagorancin Compaore.