Sulhu kan batun gudanar da zabuka a Burkina Faso
August 22, 2015Talla
Hukumar sadawar kasar ce dai ta CSC ta dauki wannan mataki na shata yarjejeniyar da ke zaman wani babban alkawari ga 'yan kasar ta Burkina Faso, wanda kuma kafofin yada labaran kasar da ma kungiyoyin fararan hulla suka rattaba wa hannu a gaban shugaban kasar na rikon kwarya Michel Kafando. Sanin kowa ne dai zabuka a Afirka na a matsayin babban abun da ke kawo rarrabuwar kanu tsakanin al'umma, inda cikin jawabinta shugabar hukumar sadarwar kasar ta Burkina Faso Nathalie Somé, ta ce wannan yarjejeniya zata bada damar gudanar da zabe wanda babu tashin hankali a cikinsa wanda kuma kowa zai aminta da shi.