1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Suu Kyi ta gamu da martanin 'yan fafutika

Yusuf Bala Nayaya
September 19, 2017

Suu Kyi dai ta yi alawadai kan take hakkin bil Adama kuma ta ce duk masu hannu a ciki zasu fiskanci shari'a sai dai 'yan fafutika sun ce ba da gaske take ba.

Myanmar Naypyitaw Aung San Suu Kyi
Hoto: Reuters TV

Kungiyoyin 'yan fafutika na kasa da kasa na ci gaba da mayar da martani ga shugabar al'umma a kasar Myanmar Aung San Suu Kyi da ta bude baki a karon farko tun bayan da soja suka shiga kisan gilla kan kabilar  Rohingya bayan hari da 'yan tawayen cikinsu suka kai a ranar 25 ga watan Agusta, lamarin da ya haifar da martanin soja mai tsauri da ya jawo sama da mutane 400,000 suka kauracewa mahalansu inda suka nemi mafaka a Bangaladash.

Suu Kyi dai ta yi alawadai kan take hakkin bil Adama kuma ta ce duk masu hannu a ciki zasu fiskanci shari'a sai dai 'yan fafutika kamar daga kungiyar Amnesty International kamar James Gomez mai kula da ofishin kungiyar a yankin Kudu maso Gashin Asiya da Pacific y a ce abin da ta fadi da ma gwamnatinta abin kunya ne gareta kuma suna ci gaba da boye-boye kan abin kazantar da sojan kasar suka aikata a jihar ta Rakhine.

Shi kuwa Phil Robertson, na kungiyar Human Rights Watch ya ce shugabar ta ce tun daga biyar ga watan Satimba soja sun tsayar da martani da suke kai wa 'yan Rohingya to amma tambayarsa ita ce wa ke ci gaba da kona garuruwan mutanen tsawon makonni biyu.