1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Sweden ta zargi Iran da kitsa tarzoma a kasarta

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 30, 2024

'yan sanda da sojojin Sweden sun fara wani aikin hadin gwiwa da kasashe daban-daban na duniya, domin dakile wannan shiri

Hoto: edna/IMAGO

Sweden ta zargi Iran da amfani da gungun 'yan dabar kasar don tayar da hankalin jama'a, ta hanyar shirya tarzomar kin jinin Isra'ila da Amurka a cikin kasar ta Sweden.

Karin bayani:Kasashen Musulmi na tir da kona al-Qur'ani

Hukumar leken asirin kasar da kuma rundunar 'yan sandan kasar sun bankado wuraren da suka ce 'yan daban na shirin durfafa, da ma mutanen da suke shirin farwa.

Karin bayani:Zaman makokin mutuwar Shugaba Ebrahim Raisi na Iran

Yanzu haka dai 'yan sanda da sojojin Sweden sun fara wani aikin hadin gwiwa da kasashe daban-daban na duniya, domin dakile wannan shiri, in ji shugaban hukumar leken asirin kasar Daniel Stenling.