SiyasaJamus
Sweden za ta sayi tankokin yaki kirar Jamus
January 9, 2025Talla
Sweden za ta sayi tankokin yaki na Jamus samfurin Leopard 2 A8 guda 44 yayin da ta ke kokarin sabunta rumbun makamanta.
Ministan tsaro Pal Jognson ya ce Stockholm na fatan kashe kimanin euro miliyan dubu biyu domin inganta tsaron kasar.
Hukumar tsaron Sweden ta sanya hannu a kan yarjejeniya da kamfanin hadakar kera makamai na Jamus da Faransa KNDS kuma ana fatan fara mika makaman daga 2028 zuwa 2031.
Daga cikin makaman za a yi amfani da tankoki goma don maye gurbin tankokin da Sweden ta bai wa Ukraine gudunmawa.
Baya ga sabbin makaman da kasar za ta sayo za kuma ta gyara wasu tankokin 66 samfurin Leopard 2 da ta ke da su.