1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Switzerland ta dena sayar wa Amurka makamai

March 20, 2026

Gwamnatin Switzerland ta yanke shawarar dena fitar da makaman yaki zuwa Amurka don cire kanta cikin masu hura wutar rikici tare da tabbataar da matsayarta na 'yan ba ruwanmu a rikicin Gabas ta Tsakiya.

Wani samfurin makamin yaki a fagen daga
Wani samfurin makamin yaki a fagen dagaHoto: U.S. Army/ABACAPRESS/picture alliance

Hukumomin kasar Switzerland ta jaddada matsayarta na cewa ba za ta ba wa kamfanonin kera makaman kasarta lasisin sayar wa Amurka makamai ba saboda cigaba da kai hare-hare a kan Iran.

Manazarta sun ce irin wannan matakin zai yi dai-dai da wajibcin shari'a na kasar Switzerland, na yin mu'amala da dukkan bangarorin daidai wa daida a cikin tashe-tashen hankula don kaucewa ba da gudunmuwar makamai zuwa yankunan da ake gwabza yaki.

Matakin ya zo ne a yayin muhawara mai zurfi a Bern kan yadda ya kamata a yi amfani da tsaka tsaki a cikin yanayin siyasar yankii da ake fuskanta a halin yanzu. Duk da cewa gwamnatin Switzerland ta sassauta wasu ka'idojin fitar da makamai don tallafawa masana'antar kera makamai na cikin gida, amma kokarin kwatanta adalci ya zama babban makasudin daukar matakin jan linzami musamman idan kara hura wutar rikice-rikice.

Switzerland ta fitar da makaman yaki na aikin soja na kusan biliyan daya na kudin kasar a shekarar 2025, kuma tare da Amurka na kan gaba cikin manyan kasashen da suka fi saya. Sai dai jami'ai sun yi gargadin cewa tsaurara matakan na haramta kai makaman Amurka zai lalata hadin gwiwar tsaro da Washington da sauran kawayenta.

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Iran, ta ce an kashe sama da mutane 1,500 an kuma kashe kananan yara 204 a Iran, yayin da mutane akalla 1,000 suka mutu a Isra'ila sakamakon fada da Lebanon.