1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Switzerland ta kwace kadarorin Maduro

Abdul-raheem Hassan
January 5, 2026

Gwamnatin Switzerland ta kwace kadarorin Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro da na mukarrabansa bayan da Amurka ta kama shi da nufin gurfanar da shi kan zargin laifukan safarar kwayoyi da ta'addanci.

Maduro - Der Unzerstörbare
Hoto: Java

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Switzerland ba ta yi karin haske kan darajar kadarorin da ta kwace ba, amma matakin ya shafi makusantan Maduro guda 37 amma bai shafi jami'an gwamnatin kasar na yanzu ba, kuma za a mayar da wasu kadarorin zuwa baitalmalin gwamnati.

Switzerland ta ce matakin zai fara aiki nan take kuma zai dau tsawon shekaru hudu da nufin hana silalewar muhimman kadarori matakin na zama kari ne kan takunkuman da ke kan Venezuela daga 2018.

Dangane da halin da ake ciki a Venezuela bayan da Amurka ta kama Maduro da mai dakinsa, Switzerland na nazari kan shiga tsakani don warware rikicin cikin lumana, musamman ta hanyar bin dokokin duniya.