1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Switzerland ta yi tayin sulhu a Kamaru

Abdoulaye Mamane Amadou
June 27, 2019

Kasar Switzerland ko Suisse ta bayyana aniyar shiga tsakani don sulhunta rikicin kasar Kamaru tsakanin gwamnati da 'yan aware na yankin Ingilishi da ke neman ballewa daga kasar. 

Kamerun Sprachenstreit um Englisch
Hoto: Getty Images/AFP


A cikin wata sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar Switzerland ko Suisse ta fitar a ranar Alhamis, ta ce bangarori da dama ne suka bukaci gwamnati ta jagoranci wata tattauanawar sulhu tsakanin bangarorin da ba sa jituwa, zuwa ga wata tattaunawa ta hakika domin samun zaman lafiya mai dorewa.

Rikicin da 'yan awaren suka shafe watanni suna tafkawa da bangaren gwamnatin Kamaru ya lamshe rayukan jama'a fiye da dubu 1.800, baya ga haddasa kaurar jama'a daga gidajensu akalla dubu 530.000.